IQNA

Bayar Da Horo Kan Fasahar Kayata Rubutun Kur’ani

23:58 - August 08, 2018
Lambar Labari: 3482874
Bangaren kasa da kasa, karamin ofishin jakadancin Iran a kasar Senegal ya dauki nauyin shirya wani horo na koyar da fasahar kayata rubutun kur’ani.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa,   karamin ofishin jakadancin Iran a kasar Senegal ya dauki nauyin shirya wani horo na koyar da fasahar kayata rubutun kur’ani mai tsarki.

Shugaban karamin ofishin jakadancin na Iran a Senegal Sayyid Hassan Ismati ne yake jagorantar shirin, inda wani adadi na matasa masu shawa’ar samun horon suke halartar wurin da ake gudanar da shirin.

Babbar manufar hakan dai ita ce kara fadada ilmimin rubutun kur’ani a tsakanin muuslmin kasar Senegal wadanda suke da tsohon tarihi a wannan fage.

Ana gudanar da shirin ne a birnin Tuba daya daga cikin muhimman biranan musuluncia  kasar Senegal, birnin da ya shahara da fitattun makaranta kur’ani da kuma manyan malaman addinin musulunci, musamman mabiya darikar muridiyyah.

3737124

 

 

 

 

 

 

captcha