Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ne bangaren kula da harkokin kur’ani na hubbaren Imam Hussain (AS) ya girmama wasu mata da suka nuna kwazo kan lamarin kur’ani a karkashin cibiyar.
Wannan mataki ya zo da nufin kara karfafa gwwar mata wajen bayar da himma a kan lamarin kur’ani mai tsarki.
A kowace shekara ana gudanar da taruka na gasa da kuma na karatun kur’ani a karkashin wannan cibiya, kamar yadda kuma akwa wasu tsare-tsaren na bayar da horon hardar kur’ani.