Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na mamlaka ya bayar da rahoton cewa, ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ta samar da makarantun kur’ani guda 6 a arewacin kasar.
Muhammad Mukhrat Juma’a ministan ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar ta Masar ya bayyana cewa, tuni wadannan makarantu suka fara gudanar da ayyukansu na koyarwa.
Ya ce babbar manufar samar da wadannan makarantu dai ita ce, kokarin kawo sabon salon a koyarwa tare da wayar da kan daliban kan hakikanin koyarwar kur’ani, domin hana akidar ta’addanci ci gaba da yaduwa awannan yanki.