IQNA

Gangamin Al’ummar Iran Domin Kalubalantar Aikin Masu Girman kai

23:52 - November 04, 2018
Lambar Labari: 3483097
Bangaren kasa da kasa, a dukkanin biranan kasar Iran al’umma sun fito domin tunawa da ranar 13 ga Aban, domin bayar da amsa ga Amurka kan hankoronta na gurgunta Iran ko ra wane hali.

Kamfanin dillancin labaran iqna, miliyoyin al'ummar sun gudanar da zanga-zangar ranar 13 ga watan Aban ranar fada da girman kan duniya inda suka bayyana cewar da yardar Allah a wannan karon ma al'ummar Iran za su yi nasara kan sabon takunkumin da gwamnatin Amurka ta sanya wa kasar.

al'ummar Iran din sun bayyana hakan ne cikin wata sanarwar bayan taro da suka fitar a karshen zanga-zangar da suka gudanar a nan Tehran da sauran garuruwa na Iran inda suka bayyana cewar: Kyama da kuma fada da girman kan duniya daya ne daga cikin koyarwar juyin juya halin Musulunci na Iran, don haka al'ummar Iran za su ci gaba da riko da wannan koyarwar har sai an kawo karshen wannan annobar musamman mulkin mallakan Amurka.

Har ila yau mahalarta zanga-zangar sun sake jaddada goyon bayan su ga al'ummomin da suke karkashin zaluncin Amurka da sahyoniyawa bugu da kari kan kungiyoyin gwagwarmaya a fadar da suke yi da ma'abota girman kan duniya. 

A safiyar yau ne miliyoyin al'ummar Iran a duk fadin kasar suka fito don raya ranar 13 ga watan Aban don girmama ranar da daliban jami'a mabiya tafarkin marigayi Imam Khumaini suka mamaye ofishin jakadancin Amurka da ke Tehran sakamakon ayyukan leken asirin da ake gudanarwa a can din.

3761259

Gangamin Al’ummar Iran Domin Kalubalantar Aikin Masu Girman kai

Gangamin Al’ummar Iran Domin Kalubalantar Aikin Masu Girman kai

Gangamin Al’ummar Iran Domin Kalubalantar Aikin Masu Girman kai

 

 

captcha