Kamfanin dillancin labaran iqna, a cikin wani bayani da ta fitar, ma’ikatar kula da harkokin addini a Masar ta ce za a bude wasu makarantun kur’ani mai tsarki guda 24 kafin karshen 2018 da muke ciki.
Bayanin ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ya ce, idan aka kammala aikin gina wadannan makarantu daga nan zuwa karshen shekara, adadin makarantun kur'ani da suke karkashin kulawar wannan ma'aikata za su kai 788.
Haka nan kuma bayanin yakara da cewa, idan aka kammala aikin gina makarantun, za a sanar da iyayen yara domin su kawo yaransu a yi rijistar sunayensu kafin lokacin fara karatu.