IQNA

An Cika Shekaru Takwas Da Fara Yunkurin Al’umma A Bahrain

23:17 - February 13, 2019
Lambar Labari: 3483368
Bangaren kasa da kasa, a ranar 14 ga watan fabrairu ne aka cika shekaru 8 daidai da fara yunkurin al’umma na neman sauyi na dimukradiyya akasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na mana post ya bayar da rahoton cewa, gungun matasa da ake kira 14 ga Fabrairu, sun gudanar da taruka a ciki da wajen kasar, domin tunawa da zagayowarlokacin da suka fara yunkurin neman sauyi na dimukradiyya.

Rahoton ya ce gungun 14 ga watan Fabrairu watsa bayai a shafukan yanar gizo da kuma kafofin yada labarai masu zaman kansu da suke wajen kasar, dangane da abubuwan da suka faru a cikin shekaru a kasar Bahrain.

A cikin wadannan shekaru da al’umma suka yi suna gudanar da harkokinsu an neman sauyi ta hanyar lumana, sun fuskanci matsi da azabtarwa da kisa da kuma dauri, kamar yadda kuma aka kori dubbai tare da haramta musu ‘yancinsu na zama ‘yan kasa.

Babbar manufar yunkurin dai ita ce, neman masarautar kasar ta bayar da dama ga al’ummar kasa su zabi ‘yan majalisar dokokin kasar da kansu ta hanyar kada kuri’a, tare da bayar da dama ga majalisar da al’umma ta zama ta zabi firayi minista, shi kuma sarki ya ci gaba da mulkinsa, amma firayi minista da majalisar ministoci za su ja ragamar harkokin gudanarwa na gwamnati, maimakon yadda lamarin yake sarki shi ne wuka shi ne nama a cikin dukkanin lamarin kasa.

Wannan bukata ta al’umma ta fukanci mummunan martani daga masarautar kasar wadda ta ginu a kan tsari na kama karya da bautar da al’umma, amma duk da hakan al’umma sun zabi neman ‘yancinsu ta hanyar lumana inda ba su taba daukar makami ko bin hanyoyi na tayar da hankali ba a yunkurin nasu.

3789735

 

 

captcha