IQNA

Jagora: Al’ummar Iran Ta Kara Karfi Ninki 40 Makiya Kuma Sun Kara Rauni

22:01 - February 26, 2019
Lambar Labari: 3483403
Bangaren siyasa, jagoran juyin juya halin muslucnia Iran ya bayyana cewa,a  cikin wadannan shekaru makiya Iran sun kara rauni, yayin da kasar ta kara karfi ninki arbain.

Kamfanin dillancin labaran iqna, A yayin da yake ganawa da wani gungu na sha'irai da ambaton iyalan gidan Anabta tsarkaka a wannan rana ta talata, da farko jagoran juyin musulinci Aya. Sayyid Aliyul-Khaminai ya bayyana farin cikinsa da wannan rana na tsagayowar ranar haifuwar diyar fiyeyyen halitta sayyida Zahra amincin Allah ya tabbata a gareta, sannan ya ce cikin shekaru 40 da suka gabata, makiya sun yi amfani da duk wani karfi da suke da shi na ganin sun cutar da juyin musulinci, amma al'ummar Iran ta hanyar dogaro da Ubangiji da kuma yin abinda ya rataya kansu, sun samu nasarar a kan makircin makiya, kuma a yanzu,al'ummar Iran din ta samu karfi fiye da lokutan da suka gabata yayin da makiyanta ke kara raunana.

Aya. Sayyid Aliyul-Khaminai ya ce tafarkin ma'abota gaskiya da ma'abota karya a yau daidai yake da tafarkinsu a zamanin fiyeyyen halittu da shugabanin shiriya tsarkaka amincin Allah ya tabbata a gare su, kuma kamar yadda a wancan lokaci duk da yawan makirci da makarkashiyar da makiya ke kullawa ta hanyar farfaganda, suka rushe, to a yau ma hakan na jiran makiyan da suka ja daga  a gaban musulinci.

Har ila yau jagoran ya kara da cewa sha'irai da masu ambaton iyalan gidan anabta tsarkaka na a matsayin taska da jari  na cimma manufofin juyin musulinci, kuma kamata ya yi ayi amfani da wannan jari wajen bayyana manufofin musulinci da sayyida Zahra gami da Imam Husain(a.s) .

 

3793421

 

 

 

 

captcha