IQNA

Zarif: Ya Kamata Amurka Ta Sake Tunani Kan Saka IRGC Cikin Kungiyoyin ‘Yan Ta’adda

22:58 - April 08, 2019
Lambar Labari: 3483531
Ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad Zarif ya ja kunnen gwamnatin Amurka kan yunkurinta na saka dakarun kare juyin juya halin muslunci na Iran a cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda.

kamfanin dilalncin labaran iqna, Zarif ya bayyana haka ne a cikin sako da ya aike ta shafinsa na twitter, inda ya ce hakika gwamnatin Amurka mai ci tana son faranta wa Netanyahu rai, da kuma tseratar da shi daga faduwa zabe.

Ya ce baya ga dukkanin hidimar da gwamnatin Trump take yi wa Netanyahu, har kuma tana tunanin saka dakarun kare juyin juya hali na kasar Iran a cikin jerin kungiyoyi da take kira na ‘yan ta’adda, ba tare da la’akari da abin da zai iya zuwa ya dawo ba.

Zarif ya ce saka wannan runduna a cikin jerin ‘yan ta’adda sakamakon yin hakan ba ai zama mai kyau ga Amurka ko kuma wadanda take yi domin su ba, saboda haka a sake yin nazari.

A ranar Juma’a da ta gabata ce jaridar Wall Street Journal ta kasar Amurka da kuma kamfanin dillancin labaran Reuters, suka bayar da rahotannin cewa, gwamnatin Trump na shirin saka dakarun IRGC a cikin jerin sunayen ‘yan ta’adda.

3802021

 

captcha