IQNA

A Gobe Za A Fara Gasar Kur’ani ta Dubai

23:41 - May 06, 2019
Lambar Labari: 3483611
Bangaren kasa da kasa, a gobe za a bude gasar kur’ani mai tsarki ta birnin Dubai.

Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na qurqn.gov.ae ya bayar da rahoton cewa, a gobe ne za a bude babbar gasar da aka fi sani da gasar kyauta ta Dubai.

Za a gudanar ad gasar nea  babban dakin taruka na birnin.

Ibrahim Muhammad Bumaliha babban darakta a bangaren hulda da jama’a na maaikatar al’adu ta kasar haddadiyar daular larabaw aya bayyana cewa, kasashe 90 nme za su halarci gasar wadda za a fara gobe.

Gasar ta Dubai a bana sabanin yadda aka saba gudanar da ita ne, inda a kan gudanar da a cikin mako na biyu an watan Ramadan, amma a bana daga ranar biyu zuwa ranar 14 ga watan na Ramadan.

Abdulkarim Ibrahim Saleh daga Masar, Amin Idris Fallata daga Saudiyya, Salim Muhammad Dubi daga UAE, Abdulhadi Likab daga Aljeriya, Ibrahim Muhammad Kishidan daga Libya, Ma’ani Sheikh Hassan Gansuri daga Burkina Faso, su ne manyan alkalan gasar.

Daga jamhuriyar muslunci ta Iran kuwa Muhammad Reza Waliy Muhammadi shi ne ai wakilci kasar a wannan gasa.

 

3809215

 

 

captcha