IQNA

Paparoma Ya Yi Allawadai Da Kisan ‘Yan Gudun Hijira A Libya

23:48 - July 08, 2019
Lambar Labari: 3483819
Shugaban mabiya addinin kirista ‘yan darika Katolika Paparoma Francis ya mayar da martani dangane da hare-haren da aka kai a kan bakin haure a Libya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a jiya a fadar Vatican, Shugaban mabiya addinin kirista ‘yan darika Katolika na duniya Paparoma Francis, ya bayyana takaicinsa dangane da kisan fararen hula ‘yan gudun hijira a kasar Libya, biyo bayan hare-haren da dakarun Haftar suka kaddamar a kansu.

Ya ce dole ne a samar da wata hanya ta kare rayukan fararen hula  a kasar Libya, musamman bakin haure wadanda hanya ta kawo su, tare da tabbatar da cewa an kare hakkokinsu da kuma nisantar daukar duk wani mataki na muzguna musu a kasar.

Haka nan kuma Paparoma ya yi addu’a ga dukkanin mutanen da akashe  akasar ta Libya sakamakon wanann hari, da ma mutanen da aka kashe sakamakon hare-haren ta’addanci a cikin wannan makoa  kasashen Afghanistan, Mali, Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar.

Ministan harkokin cikin gida na kasar ta Libya Fathi Bashaga ya bayyana cewa, hare-haren da aka kaddamar kan sansanonin bakin haurea  kusa da birnin Tripoli, jiragen yakin kasar UAE samfurin F-16 da suke mara baya ga Haftar ne suka kaddamar da hare-haren.

Majalisar dinkin duniya, gami da kungiyar tarayyar turai da kungiyar tarayyar Afrika, duk sun yi Allawadai da kakakusar murya dangane da harin, tare da yin kira da a gudanar da sahihin bincike kan lamarin.

 

3825224

 

captcha