IQNA

Shirin Isra’ila Na Kwadaitar Da Kasashe Kan Maida Ofisoshin Quds

22:52 - July 28, 2019
Lambar Labari: 3483889
Bnagaren kasa da kasa, Isra’ila na shirin yin amfani da kudade domin kwadaitar da wasu kasashe domin su mayar da ofisoshin jakadancinsu zuwa birnin Quds.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Palestine ya bayar da rahoton cewa, Yara’il Katez ministan harkokin wajen Isra’ila ya bayar da shawar cewa, Isra’ila ta bayar da kudade da suka kai Shekel miliyan 50 na Isra’ila, ga dukkanin kasashen da suka dauke ofisoshin jakadancinsu zuwa Quds.

Jaridar Isra’ila ta Isra’el Human ta rubuta cewa, ministan harkokin wajen na Israila yana niyyar kafa wani kwamiti kan wannan batu.

Haka nan kuma an nakalto daga gare shi yana fadar cewa, batun mayar da ofisoshin jakadancin kasashen duniya zuwa birnin Quds batu ne na siyasa mai matukar muhimamnci ga Isra’ila da al’ummar yahudawa.

Shugaban Amurka Donald Trump shi ne ya fara dauke ofishin jakadancin Amurka daga zuwa Quds

A ranar 21 ga watan Disamban 2017, majalisar dinkin duniya ta kada kuri’ar kin amincewa da wanna shiri, tare da kiran kasashen duniya su yi watsi da shi.

3830624

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha