Kamfanin dillancin labaran iqna, za a gudanar da taron bayar da horo akan kur’ani mai tsarki da addinin muslunci a jihar Maryland ta kasar Amurka.
Wanda zai jagoranci wannan bayar da horo shi ne Wasim Khan, wanda zai yi amfani da kur’ani wajen gabatar da mafi yawan abubuwan da za a koyar.
Haka nan kuma za a koyar da wasu darussa da suka hada akidojin addini gami da matsayin annabawa a cikin addinin muslunci.
A halin yanzu dukkanin wadanda za s hakarci wannan horo sun fara gabatar da sunayens domin a san da su, kamar yadda kuma horon zai gudana nea cikin masallacin musulmin yankin.