IQNA

Ministan Lafiya Na Yemen: Tsare Jiragen Ruwa Na Mai  Zai Jefa Marassa Lafiya Cikin Hatsari

23:52 - October 06, 2019
Lambar Labari: 3484125
Bangaren kasa da kasa, ministan lafiya na kasar Yemen ya ce ci gaba da tsare jiragen ruwa na mai zai jefa dubban marassa lafiya cikin hatsari.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga tashar almayadeen cewa, Taha Mutawakil ministan lafiya na kasar Yemen ya ce ci gaba da tsare jiragen ruwa na mai da ke kan hanayrsu zuwa Yemen da kawancen saudiyya ke, zai jefa dubban marassa lafiya cikin hatsarin gaske.

Ya ce a halin yanzu akwai dubban marassa lafiya wadanda rayuwarsu ta ta’allaka ne da samun mai a kasar domin amfanin na’urorin da ake yi musu ayyyuka a asibtoci, wanda rashin hakan ke nufin cewa za su iya rasa rayuwarsu a kowane lokaci.

Hakan na kuma ministan na Yemen ya bayyana cewa,a  halin yanz akwai manyan jiragen mai guda tara dauke da man fetur da kawance Saudiyya ya hana su isa gabar ruwan Yemen, da nufin ci gaba da jefa al’ummar kasar cikin kunci.

 

 

 

 

http://iqna.ir/fa/news/3847852

 

 

captcha