Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, yanzu haka ana shirin fara gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasar Qatar da aka saba gudanarwa a kowace shekara.
Bayanin ya ce dukkanin mahalrta wannan gasa dai daliban makamarantu ne, kamar yadda kuma adadin wadanda za su kara da juna a gasar zai kai dalibai 290.
Babbar manufar gasr dai ita ce karfafa gwiwar matasa masu sha’awar shiga harkokin kur’ania kasar domin su ci gaba da kara bayar da himma.
Za a gudanar da gasar a bangaren harda da zai hada da izihi na 10, sai kuma izihi na 15, da kuma na 20 zuwa na 25, daga karshe kuma za a karrama dukkanin wadanda suka nuna kwazo a gasar.