Kamfanin dillancin labaran IQNA, Hussain Amir Abdollahian babban mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar Iran kan harkokin kasa da kasa ya bayyana cewa; ‘yan ta’addan daesh sun sake dawowa amma a cikin fararen kaya na al’ummar Iraki.
Ya bayyana hakan ne a cikin shafinsa na twitter jim kadan bayan wani hari da aka kai kan karamin ofishin jakadancin Iran da ke birnin Najaf.
Ya e a fili yake kan cewa Amurka da Saudiya da kuma Isra’ila ne suke da hannu wajen daukar nauyin dukkanin abin da yake faruwa a Iraki na ta’addanci, amma a wannan karon ‘yan ta’addan da wadannan kasashen suke yin amfani da su sun sake bayyana ne amma a cikin farin kaya.