IQNA

Kimanin Mutane Dubu 6 Ne Ke Zuwa Duba Wani Dadadden Kur’ani A China

17:28 - December 01, 2019
Lambar Labari: 3484283
Bangaren kasa da kasa, kimanin mutane dubu 6 ne dai suke duba wani kur’ani da aka ajiye a dakin kayan tarihi a China.

Kamfanin dillancin labaran iqna, wanann kur’ani an rubuta shi tsakanin karni na 11 zuwa na 13 kuma an ajiye shi a wani wuri na adana kayan tarihi.

Yana da shafuka 867 a cikin bangarori guda 30, kamar yadda aka rarraba juzuoinsa, haka nan kuma yana da nauyi da ya kai kligram 13.

Tun a cikin shekara ta 2007 ce dai aka gyara wannan kwafin kur’ani aka saka shia  cikin wani gilashi, wanda dubban mutane da dama suka zuwa wurin suna dubawa a kowace rana a akasar ta China.

 

3860768

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha