IQNA

Mata Musulmi Masu Lullubi Suna Taka Rawa A Fagen Wasanni A Amurka

14:16 - December 11, 2019
Lambar Labari: 3484310
Bangaren kasa da kasa, mata muuslmi masu hijabi suna taka rawa a bangaren wasanni a kasa Amurka.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, a daidai lokacin da ake wasannin share fagen shiga wasannin motsa jiki na 2020 a Tokyo Japan, mata musuli masu lullubi suna taka muhimmyar rawa a fagen wadannan wasani a kasar Amurka.

Duk da cewa da dama daga cikinsu suna kokawa kan yadda suke fuskantar matsin lamba sakamakon lullubin da suke sakawa, duk kuwa da ewa da dama daga cikinsu sun tsallake kuma sun samu cancantar shiga wasannin.

Wata musulma mai suna Nu Elexendria Abu Akram yar shekaru 16 da haihuwa, ta bayyana cewa, ta samu cancantar zuwa wasanin na motsa jiki na duniya, amma tana fuskantar matsin lamba sakamakon saka lullubi da take yi.

Mata musulmi da dama suna shiga wasanni a kasar Amurka bangarori daban-daban, musamamna  bagaren kwallon kwado, da kuma gudu da sauran wasanni na tsalle-tsalle.

 

3863310

 

captcha