IQNA

Zaman ISESCO Na Sha Daya A Tunisia / Bahasi Kan Siyasar Musulunci

22:41 - December 14, 2019
Lambar Labari: 3484317
Bangaren kasa da kasa, Taron ISESCO a kasar Tunisia tare da halartar Abu Zar Ibrahimi Torkaman.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, an shirya gudanar da zaman taron kungiyar raya al’adun muslunci ta ISESCO a birnin Tunis na kasar Tunisia, wanda Muhammad Zainul abiding ministan al’adu na Tunis, da Muhammad Salim Malik shugaban kungiyar suka kira a cikin wannan mako.

Wannan taro dai zai samu halartar manyan jami’an gwamnatoci na kasashen musulmi da suka hada ministocin al’adu, da kuma masana kan harkokin siyasar kasashen musulmi, kamar yadda wakilan wasu kungiyoyi na kasa da kasa za su halarci taron.

A karshen zaman taron za a zabi birnin Tunis a matsayin birnin al’adun muslunci na wannan shekara.

Abin tuni dai a shekara ta 2017 da ta gabata, an gudanar da irin wanann zaman taro a Khartum, inda akazabi birnin a matsayin birnin al’adun musulunci.

3863865

https://iqna.ir/fa/news/3863865

 

 

 

 

captcha