IQNA

Babban Taron Mabiya Mazhabar Shi’a Na Kasar Ghana

11:46 - December 22, 2019
Lambar Labari: 3484336
Mabiya mazhabar shi’a na kasar Ghana za su gudanar da babban taronsu na yin bita a 2020.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, mabiya mazhabar shi’a a kasar Ghana za su gudanar da babban taronsu na karo na biyu domin yin bitar aikace-aikacensu a shekara ta 2020 a kasar Ghana.

Shugaban mabiya mazhabar shi’a  a kasar Ghana Sheikh Abubakar Kamaluddin ne zai jagoranci taron, tare da halartar wasu malamai na kasar gami da wasu manyan jami’an gwamnatin Ghana, da uma wakilan kungiyoyin addini a kasar.

Taron zai gudana ne a babban jami’ar musulunci ta kasar Ghana da ke birnin Accra fadar mulkin kasar.

A yayin taron mabiya mazhabar shi’a za su bayyana irin tsare-tsaren ayyukansu da kuma abubuwa da suke da zimmar aiwatrwa a cikin shekara ta 2020 a dukkanin bangarorin.

 

https://iqna.ir/fa/news/3865596

captcha