IQNA

Gasar Karatu Da Hardar Kur’ani Mai Tsarki Ta Kasar Libya

0:51 - December 25, 2019
Lambar Labari: 3484341
Ana shirin fara gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta kasar Libya ta shekara-shekara.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin www.218tv.com ya bayar da rahoton cewa, Ana ta shirin fara gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta kasar Libya da ake gudanarwa a garin Khums, inda a halin dukkanin shirye-shirye sun kammala.

Bayanin ya ce wanann gasa na daga cikin irin ta masu matukar muhimmanci da ake gudanarwa  a kasar ta Libya a kowace shekara, wadda ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar take daukar nauyinta.

Kamar dai yadda aka saba ana gudanar da gasar ne tare da halartar daliban makarantun kur’ani, da suka hada da makarata da kuma mahardata kur’ani mai girma na larduna.

 

https://iqna.ir/fa/news/3866251

 

 

 

 

captcha