IQNA

‘Yan Majalisa 170 A Iraki Sun Amince A Fitar Da Sojojin Amurka daga kasarsu

23:37 - January 05, 2020
Lambar Labari: 3484379
‘Yan majalisar Iraki 170 ne suka amince da daftarin kudirin fitar da sojojin Amurka daga kasa wanda yanzu ya zama doka.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, a wani zama na musamman da majalisar dokokin kasar Iraki ta gudanar a yau Lahadi, kimanin yan majalisa 170 ne suka rattaba hannun a daftarin kudirin neman ficewar sojojin Amurka daga kasar.

Wannan na zuwa ne bayan harin Amurka a kasar da ya yi sanadiyar shahadar Janar Qasim Sulaimani kwamandan dakarun Qudus ,da kuma Abu Mahdi Al’ Muhandis mutum na biyu a kungiyar Hashdu’sha’abi ta kasar Iraki.

Daftarin kudurin ya kunshi abubuwa guda Uku kamar haka

1 - wajibi ne gwamnatin kasar ta yi watsi da duk wani neman taimako daga dakarun hadin gwiwa domin yakar kungiyar ta’adda ta Daesh domin an kawo karshen yaki a kasar, tun da an yi nasara akan dakarun kungiyar, don haka dole ne gwamnatin ta kori dukkan dakarun kasashen waje da ke kasar.

2 - dole ne gwamnati da babban hafsan hafsoshin sojin kasar su sanar da lokaci da wurin zaman sojojin da ake bukata domin bada horo ga dakarun kasar a Iraki.

3 - haka zalika dole ne gwamnati karkashin ma’aikatar harkokin waje ta shigar da kara gaban Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya game da keta hurumi da tsaron kasar da Amurka ta yi .

4 - wannan kuduri zai fara aiki nan take  bayan amincewa da shi a majalisar dokokin kasar ta Iraki.

3869380

 

captcha