IQNA

Zaman Taro Mai Taken Shiriyar Kur’ani a Sudan

23:46 - January 10, 2020
Lambar Labari: 3484402
An fara gudanar da wani zaman taro na kasa da kasa mai taken shiriyar kur’ani a kasar Sudan.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, a jiya ne aka fara gudanar da wani zaman taro na kasa da kasa mai taken shiriyar kur’ani mai tsarki a birnin Khartum fadar mulkin kasar Sudan  tare da hadin gwiwa tsakanin jami’an Afrika da kuma Ummul ura da ke Makka.

Bayanin ya ci gaba da cewa, tarin yana samun halatar masana daga kasashen msusulmi daban-da hakan ya hada da kasashen larabawa da kuma na afrika.

Jakadan kasar Saudiyya a Sudan Ali Bin Hassan Jaafar na daga cikin wadanda suke jagorantar taron, da kuma shugaban jami’ar Ummul Kura da ke Makka Yahya Alzamzami.

Alzamzai na daga cikin wadanda suka fara gabatar da jawabi, kamar yadda kuma masana daga kasashen musulmi da suke halartar taron suke gabatar da na makaloli.

 

https://iqna.ir/fa/news/3870493

 

 

 

captcha