Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin yada labarai na sabaq ya bayar da rahoton cewa, Najat Falu Bilqasim tsohuwar ministar ilimi mai zurfi a kasar Faransa, wadda ‘yar asalin kasar Morocco ce, ta bayyana cewa koyar da kur’ani a makarantu a Faransa ya zama wajibi.
Tsohuwar ministar ta bayyana hakan nea wata zantawa da tashar RTL ta kasar faransa, inda ta ce kyamar addinin musulunci na karuwa cikin sauri a Faransa.
Bilaqsim ta ce wannan na faruwa ne sakamakon rashin masaniya kan addinin muslunci a tsakanin mtanen kasar Faransa, kamar yadda ta bayyana saka hijabi a matsayin ‘yanci ne na addini.
Ta ce koyar da kur’ani zai taimaka wajen rage kyamar addinin muslunci a kasar, kamar yadda kuma ta bukaci da a janye dokar hana mata saka hijabia wuraren ayyuka ko makarantu.