Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin yada labarai na khbrpress ya bayar da rahoton cewa, a jiya an kame mutumin da ya kona kwafin kur’anai a masallacin garin basbita da ke cikin gundumar Qasrain.
Mutumin mai shekaru 33 da haihuwa a duniya, ya fito daga gidan kaso ba da jimawa ba bisa zarginsa da aikata wasu laifuka, ida uma ya sake tafka wani laifin na kone kur’ani mai tsarki.
Bayan gudanar da bincike a gidansa, an gano wasu kwafin kur’ani da yak eta, kamar yadda kuma ya amsa cewa shi ne ya kona kur’anai a masallacin Basbita akwanakin baya.