IQNA

Kulla AlakaTsakanin Sudan Da Isra’ila Cin Amanar Allah Da Manzonsa Ne

23:33 - February 06, 2020
Lambar Labari: 3484490
Abdulhay Yusuf daya daga cikin manyan malaman addini na kasar Sudan, ya bayyana ganawar Al-Burhan da Netanyu a matsayin ha’inci.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin yada labarai na arabi 21 ya bayar da rahoton cewa, sheikh Abdulhay Yusuf shugaban bangaren binciken ilimin addinin musulunci na jami’ar Afrika da ke Sudan, ya caccaki gwamnatin kasar ta Sudan, kan hankoron da take na neman kulla alaka da Isra’ila.

Sheikh Abdulhay wanda mamba ne na kwamitin fikihu na malaman muslunci na duniya, ya bayyana ganawar da ta gudana tsakanin shugaban majalisar koli ta mulkin kasa a Sudan Abdulfattah Al-Burhan da shugaban gwamnatin yahudawa Netanyahu, da cewa hakan cin amanar addini ne.

Ya ce Al-Burhan wanda ya zo kan mulki ta hanyar juyin mulki na soji, yay i gaban kansa ne wajen karkata ga yahudawa, amma ba tare da amincewa al’ummar kasar Sudan ba.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3876430

captcha