IQNA

Ana Daukar Kwararan Matakai Kan Jami’ai A Masar Masu Sukar Siyasar Sisi

22:40 - February 14, 2020
Lambar Labari: 3484521
Gwamnatin Masar ta fara daukar kwararan matakai kan jami;anta masu sukar shirin yarjejeniyar karni.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin Alarabi jaded cewa, tun daga shekara ta 2014 ce Alsisi ya fara daukar matakan tsige jami’an diflomasiyya na kasar bayan da ya yi gwamnatin Mursi juyin mulki.

Bayanai daga ma’aikatar harkokin wajen Masar sun ce ana daukar matakai na takurawa a kan jami’an ma’aikatar da suka hada da jakdun kasar a kasashen ketare, kan yadda suke nuna rashin gamsuwa da yadda gwamnatin Al-sisi ta mika wuya bori ya hau, dangane da shirin Trump a kan falastinu da ake kira da yarjejeniyar karni.

Bayanin ya ce an kirayi jakadu da manyan mashawata na ma’aikatar harkokin wajen Masar, inda aka ja musu kunnuwa, kan su yi shiru da bakinsu kan matakin da gwamnatin kasar ta dauka na mara baya ga Trump kan shirinsa dangane da falastine da kuma makomar falastinawa.

Bisa ga wannan rahoto, an sheda wa jami’an cewa za su iya fuskantar matsala a aikinsu, da hakan ya hada da korarsu, ko kuma rage musu matsayi, ko kuma hana su wasu hakkokinsu na aiki.

 

https://iqna.ir/fa/news/3878714

 

captcha