IQNA

Falastinawa Sun Bukaci A Dauki Mataki Na Doka Kan Laifukan Isra'ila

23:56 - February 15, 2020
Lambar Labari: 3484524
Bangaren kasa da kasa, Falastinawa sun bukaci a gurfanar da Isra'ila kan laifukan yakin da take tafkawa kan al'ummar falastine.

Kamfanin dillancin labran IQNA, shafin yada labaran Alwifaq ya bayar da rahoton cewa, kwamitin bin kadun lamurran Falastinawa da keta hurumin dokokin kasa da kasa a Falastinu ya bukaci da a gurfanar da jami’an gwamnatin Isra’ila kan laifukan yaki da suke tafkawa a yankin.

Bayanin ya ce kotun duniya ta amince da a gudanar da bincike a kan bayanan da kwamitin ya gabatar mata kan laifukan yakin da gwamnatin yahudawan Isra’ila take tafkawa kan al’ummar falastinu.

Daga cikin laifukan akwai kisan fararen hula, da cin zarafinsu, da kuma keta alfarmar mata da muzgunawa kananan yara, har da kame s da tsarea  cikin gidajen kuruku ana azabtar da su.

Bayan ga haka kuma a lokuta daban-daban Isra’ila tana kaddamar da hare-hare ta sama da kasa a yankunan falastinawa, tare da rusa masallatai da cibiyoyin ilimi da na kiwon lafiya da kasuwanni gami da masallatai, wanda hakan duk yana daga cikin laifukan yaki da ya kamata a hukunta jami’an gwamnatin yahudawan a kansu a cewar kwamitin.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3878894

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha