Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, gwamnatin Sudan ta cimma yarjejeniya tare da babban kamfanin jirage a yankin Latin Amurka na LATAM, kan yin amfani da sararin samaniyar Sudan domin zuwa Isra’ila.
Bisa ga wannan yarjejeniya da aka cimmawa, tsawon tafiyar da jirage suke yi daga latin Amurka zuwa Tel aviv, ko kuma akasin hakan, zai ragu matuka.
Tun a kwanakin baya ne firai ministan Isra’ilaBenjamin Netanyahu tare da shugaban majalisar shugabancin kasar Sudan suka cimma matsaya kan kyautata alaka tsakanin Sudan da kuma Isra’ila, a wata ganawa da suka yi a kasar Uganda.
LATAM shi ne kamfanin jirage mafi girma ayankin latin Amurka baki daya, wanda yake da jirage da suke safara da yawansu ya haura 300, da suke zirga-zirga a kasashen duniya.