IQNA

Dakarun Hizbullah Dubu 25 Sun Shiga Cikin Masu Ayyukan Yaki Da Corona A Lebanon

22:48 - March 26, 2020
Lambar Labari: 3484660
Tehran (IQNA) dakarun kungiyar Hizbullah kimanin dubu 25 ne suka shiga cikin ayyukan yaki da yaduwar cutar corona a fadin kasar Lebanon.

Jaridar Qods Alarabi ta bayar da rahoton cewa, dakarun kungiyar Hizbullah kimanin dubu 25 ne suka shiga cikin ayyukan yaki da yaduwar cutar corona, tare da kafa asibitocin tafi da gidanka da kayayyakin aikin kiwon lafiya a kasar Lebanon.

Sayyid Hashim Safiyuddin, shuban kwamitin gudanarwa na kungiyar Hizbullah ya bayyana cewa, yaki da annobar corona yaki ne na hakika, a kan hakan akwai bukatar mayaka su shiga cikin lamarin domin su sadaukarwa wajen taimaka ma al’umma.

A lokacin da yake zantawa da tashar Almanar, Sayyid Safiyuddin ya bayyana cewa, dukkanin ayyukan da kungiyar za ta aiwatar zai kasance karkashin gwamnatin kasar Lebanon ne, da kuma ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar.

Kididdigar baya-bayan nan ta nuna cewa, mutane 333 ne suka kamu da cutar a Lebaon, 6 daga cikinsu sun rasa rayukansu.

 

3887496

 

 

 

captcha