Sayyid Abbas Musawi kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran a lokacin da yake ya mayar da martani dangane da take-taken Amurka cikin kasar Iraki ya bayyana cewa, abin da kasar Amurka take yi a halin yanzu a cikin Iraki ya sabawa dukkanin kiraye-kirayen da majalisar dinkin duniya da sauran bangarorin kasa da kasa suke yi, kan wajabcin nisantar duk wani tashin hankali a ko’ina cikin dunya, domin fuskantar corona.
Ya ce Amurka ba ta mutunta gwamnatin Iraki balantana al’ummarta, domin kuwa wakilan al’ummar Iraki a majalisar kasar sun kada kuri’ar da ke nemen ficewar Amurka daga kasar, amma tana ci gaba da yin biris da wannan kira.