IQNA

Ana Sa Ran Samun Ci Gaba Kan batun Maganin Corona

23:57 - April 06, 2020
Lambar Labari: 3484684
Tehran (IQNA) hukumar lafiya ta duniya ta ce ana sa ran samun ci gaba cikin sauri kan batun samun maganin corona a cikin wannan mako.

Shugaban hukumar lafiya ta duniya ya bayyana cewa, akwai yiwuwar samun gagarumin ci gaba a cikin wannan mako a yunkurin samar da magananin corona.

Ya ce kasashen duniya da dama sun dukufa  akan wannan batu, kuma akwai alamun samun nasara bisa ga irin magungunan da ake samarwa da kuma gwaje-gwajen da ake yi a kansu.

Ya kara da cewa ya zuwa yanzu kasashe kimanin 70 ne suke taimaka ma hukumarsa a wannan fage, kuma ana samun gagarumin ci gba cikin sauri.

Ya kara da cewa babban abin da ke da muhimmani a halin ci gaba da kiyaye abubuwan da jami’an kiwon lafiya suke fadi kan dalilke yaduwar cutar.

3889720

 

captcha