IQNA

Wata Tsohuwa ‘Yar Shekaru 98 Ta Hardace Kur’ani A Saudiyya

23:42 - May 13, 2020
1
Lambar Labari: 3484791
Tehran (IQNA) Samra’a Muhammad Zafer Al’umairi Al-shuhari toshuwa ce ‘yar shekaru 98 da ta hardace kur’ani mai tsarki a  kasar Saudiyya.

Tashar alarabiyya ta bayar da rahoton cewa, daya daga cikin abubuwa na ban mamaki da suka faru a wanannshekara shi ne, yadda Samra’a Muhammad Zafer Al’umairi Al-shuhari toshuwa ce ‘yar shekaru 98 da ta hardace kur’ani mai tsarki.

Sa’ad Bin Said dan wannan mata ne, ya kuma bayyana cewa tun yana karamin yaro ya fara hardar kur’ani kuma cikin karamin lokaci ya samu damar hardacewa, amma lamarin ya yi wahala ga mahaifiyarsa.

Ya ce sun yi amfani da salon a daukar wasu ayoyi da suke hardacewa  arana, wanda hakan ne ya saukaka musu hardar kur’ani.

Dangane da mahaifiyarsa kuwa ya bayyana cewa, ta yanke  kauna kan cewa da wuya ta hardace kur’ani, amma a halin yanzu da tsufa ya kamata , ta koma harda kuma cikin ikon Allah ta kamma hardar ba tare da fuskantar wata matsala ba.

 

3898600

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Rabiu Tijjani
0
0
Salam... Jama'a ku tayani da addu'a, nima na haddace al-Qur'an. Na gode, kuma Allah ya biya naku bukatun.
captcha