IQNA

A Najeriya An Sassauta Wasu Dokoki Kan Gudanar Da Tarukan addini

23:56 - June 03, 2020
Lambar Labari: 3484859
Tehran (IQNA) gwamnatin Najeriya ta sanar da sassata wasu daga cikin dokokin da aka kafa da ska shafi tarukan addini sanadiyyar bullar cutar corona.

Jaridar Premium Times ta Najeriya ta bayar da rahoton cewa, Boss Mustapha sakataren gwamnatin tarayya ya bayyana cewa,

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya janye dokar hana gudanar da ibada a masallatai da coci da gwamnati ta saka domin dakile yaduwar Korona a kasar

Hakan ya faru ne sakamakon shawarwarin da kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar annobar Korona ya ba wa Shugaba Buhari da kuma matakan da gwamnoni suka dauka na hana yaduwar cutar a fadin jihohin kasar.

” Daga yau Talata 2 ga watan Yuni za a bude Masallatai da coci coci domin gudanar da aiba kamar yadda aka saba masallaci yin salloli da kuma coci kamar yadda aka saba a da. kuma Za a ci gaba da haka daga 2 ga wata zuwa 29 ga wanan watan da muke ciki

Buhari ya ce bayan cikar makonni hudu da aka dage dokar da ta bawa jama’a damar halartar wuraren ibada gwamnati za ta sake duba yadda mutane suka yi biyayya ga umarni da dokokin da gwamnati ta sanya domin ganin irin mataken da zata dauka a gaba.

 

 

3902850

 

captcha