IQNA

Kasashen Musulmi Za Su Gudanar Da Zama kan Shirin Isra’ila Na Mamaye Yankunan Falastinawa

23:57 - June 08, 2020
Lambar Labari: 3484876
Tehran (IQNA) kungiyar kasashen musulmi za ta gudanar da zaman gaggawa domin tattauna batun shirin Isra’ila na mamaye yankunan Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan.

Shafin yada labarai na Al-shuruq News ya bayar da rahoton cewa, a ranar Laraba mai zuwa kasashen musulmi za su gudanar da zaman gaggawa domin tattauna batun shirin Isra’ila na mamaye yankunan Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan tare da hade su da sauran yankunan da ta mamaye.

Taron dai zai samu halartar ministocin harkokin waje ne na kasashe mambobi a kungiyar, wanda za a gudanar ta hanyar hotunan bidiyo ta yanar gizo.

A farkon wata mai kamawa ne dai Isra’ila ta sanar da cewa za ta hade yankunan Falastinawa na yammacin Kogin Jordan, wadanda majalsar dinkin dniya ta ayyana su a hukmance a shekara ta 1967 a matsayin yankunan Falastinawa ne da Isra’ila ba ta hakki a cikinsu.

 

3903600

 

 

captcha