A cikin bayanin da kungiyar tarayyar turai ta fitar kan shirin Isr’aila na mamaye sauran yankunan Falastinawa da ke gabar yammacin kogin Jordan, ta bayyana cewa ba za ta taba amincewa da hakan ba.
Bayanin kungiyar tarayyar turai ya ce abin da Isra’ila ke shirin yi, ya yi hannun riga da dukkanin dokoki na kasa da kasa, a kan haka kasashen tarayyar turai za su kalubalanci wannan shiri na Isra’ila na mamaye yankunan Falastinawa.
A yau ne ministan harkokin wajen kasar Jamus Heiko Maas zai isa birnin Tel Aviv domin ganawa da Netanyahu da wasu daga cikin jami’an gwamnatin yahudawan Isra’ila kan wannan batu.
A kwanakin baya dai tarayyar turai ta yi barazanar kakaba wa Isra’ila takunkumi, matukar dai ta aiwatar da shirin nata na mamaye yankunan Falastinawa yammacin kogin Jordan.