IQNA

An Kaddamar Da Kwamitin Koyar Da Karatu Ta Hanyar Yanar Gizo A Jami’ar Kur’ani Ta Sudan

23:53 - June 20, 2020
Lambar Labari: 3484910
Tehran (IQNA) an kaddamar da kwamiti da zai gudanar da ayyukan  koyar da karatun kr’ani ta hanyar yanar gizo a jami’ar kur’ani ta Sudan.

Shafin yada labarai na alnilin.com ya bayar da rahoton cewa, a yau an kaddamar da wani kwamiti wanda zai gudanar da ayyuka na musamman wajen koyar da karatun kur’ani ta hanyar yanar gizo a jami’ar kur’ani ta Sudan.

Abubakar Abdulbanat Adam Ibrahim shugaban jami'ar kur'ani ta kasar Sudan ya bayyana cewa, sun samu izinin yin hakan daga mahukunta, kuma shiri ne wanda za a fara aiwatar ad shi ba da jimawa ba.

wannan shiri dai an da nufin yin amfani da hanyoyi an zamani na yanar gizo da kuma yin amfani da na'urorin kwamfuta najami'ar domin aiwatar da wannan shiri.

Bisa ga bayanin jami'ar, shirin zai amfanar da jama'a matuka musammana  irin wannan lokaci da ake amfani da hanyoyi an zamani domin isar da ilmomi cikin sauki.

 

 

 

3905670

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: sudan
captcha