Shafin yada labarai na Hizbullah yasanar da cewa, a cikin sabon sakonsa, babban sakataren kungiyar Hizbulallah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, za su iya mayar da martani a duk inda suke bukata a cikin Isra’ila ba tare da wani shayi ba, matukar dai Isra’ila ta nemi yin wani shiahigi a kan kasa Lebanon.
Ya ce a halin yanzu kungiyar Hizbulah ba wai kawai za ta kai hari a cikin birnin Telaviv ba ne, za ta iya kai hari a duk inda take bukata a cikin Isra’ila.
Sayyid Nasrullah ya ce Isra’ila tana hankoron ganin ta kawo cikas ga karfin makaman Hizbullah, ya ce an riga an wuce wannan batun a halin yanzu.