IQNA

Bikin Cikar Shekaru 12 Da Bde Lambun Kur’ani A Kasar Qatar

22:36 - September 20, 2020
Lambar Labari: 3485201
Tehran (IQNA) an gudanar da bikin cikar shekaru 12 da bude lambun kur’ani a kasar Qatar.

Jaridar Alsharq ta bayar da rahoton cewa, a yau ne aka cika shekaru 12 da bude lambun kur’ani a kasar Qatar, inda aka yi biki ta yanar gizo tare da halartar mutane daga kasashen duniya.

Wannan lambu dai an bude shi da nufin raya sha’anin kur’ani, inda aka shuka tsirrai da dama daga cikin tsirran da aka ambata  acikin kur’ani mai tsarki domin a gan su a zahiri.

Baya ga haka kuma lambun yana daga cikin wurare da suke daukar hankula masu ziyaratar kasar, inda  a halin yanzu yan adaga cikin muhimman wurare na bude ido a kasar.

Gwamnatin kasar Qatar wadda za ta dauki nauyin bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa a shekara ta 2022, ta sanya wannan lambu ya zama daya daga cikin wuraren da za a baiwa muhimamnci tare da kayata su.

3924002

 

 

captcha