IQNA

Majami’ar Kiristoci Ta Bayar Da Taimako Domin Gyara Masallaci A Najeriya

23:18 - September 25, 2020
Lambar Labari: 3485216
Tehran (IQNA) wata majami’ar kiristoci a garin Kaduna na Najeriya ta bayar da taimako domin gyara wani masallaci da gobara ta yi wa barna.

Shafin Tribune Online ya bayar da rahoton cewa, wata majami’ar kiristoci ta bayar da taimako domin gyara wani masallaci da gobara ta yi wa barna a garin Kaduna na Najeriya.

Yohanna Buru babban malamin wannan majami’a ya bayyana cewa, ya zama wajibi a rika yin taimakekeniya tsakanin musumi da kirista a cikin dukkanin lamurra na zamantakewar al’ummar Najeriya.

Ya ce musulmi da kirista suna rayuwa da juna tsawon shekaru, kuma dukkaninsu suna bin addinai ne da aka saukar daga sama da suke dauke da sako na zaman lafiya da aminci da girmama dan adam da kuma jin kansa.

A kan haka ya ce babu wani dalili da kirista zai kalli musulmi a matsayin makiyinsa, kamar yadda musulmi ma baya kallon kirista a matsayin makiyinsa, saboda haka dole ne a karfafa alaka tsakanin mabiya wadannan manyan addinai na duniya guda biyu.

Dangane da taimakon da majami’ar kiristoci ta bayar domin gayara masallacin da gobara ta yi wa barna a unguwar Tudun Wada da ke birnin Kaduna, Yohanna Buru ya bayyawa cewa, masallaci wurin ibada ne ga Allah wanda musulmi suke yin ayyukan bautar Allah a cikinsa.

 

3925228

 

 

captcha