Jakadan MDD na musamman kan kare hakkin bil’adama a yankunan Falasdinawa da aka mamaye ya bukaci haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) ta dakatar da rushe-rushen gidajen Falasdinawa a yankunan su da ta mamaye.
Kamfanin dillancin labaran Spotnik na kasar Rasha ya nakalto Evan Haily ya na fadar haka a ranar Alhamis da dare. Ya kuma kara da cewa a shekara ta 2020 da muke ciki, HKI ta fi rusa gidajen Falasdinawa a baya-bayan nan.
Har’ila yau Stéphane Dujarric kakakin babban sakataren MDD ya bayyana cewa rushe-rushen da HKI ta yi a wannan shekarar a kasar Falasdinu da aka mamaye yana damun majalisar. Don haka ya bukaci HKI da dakatar da hakan.
Rohotannin MDD dai, sun tabbatar da cewa gwamnatin yahudawan Sahyoniyya sun rusa gidajen Falasdiwa 689 a yankin yammacin kogin Jordan da kuma birnin Quds kadai a cikin wannan shekara ta 2020 da muke ciki, inda ta bar Falasdinawa kimani 869 basu da wurin zama.