IQNA

Tattaunawar Kasashen Turai Kan Ayyukan Ta’addanci Da Suke Dangantawa Da Musulunci

23:54 - November 10, 2020
Lambar Labari: 3485353
Tehran (IQNA) manyan shugabannin turai za su gudanar da wani taro a yau, domin yaki da abin da suka kira tsatstsauran ra’ayin addinin musulunci.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, majiyoyin kungiyar tarayyar turan sun bayyana cewa, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, da kuma shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Markel sun kirayi taro a yau, domin tattauna yadda za su fusaknci abin da suke kira tsatsauran ra’ayin muslunci a cikin kasashen turai.

Zaman taron zai kunshi shugabannin na Faransa da Jamus da kuma Austria, kamar yadda manyan jami’ai na kungiyar tarayyar turai da suka hada da babban kwamishina na kungiyar, za su halarci zaman taron.

A cikin lokutan baya-bayan nan dai kyamar addinin muslunci na karuwa a cikin kasashen turai, inda wasu masu adawa da muslunci suka kona kur’ani a kasashen Sweden da kuma Denmark, kamar yadda kuma jaridar Charlie Hebdo ta ci gaba da yada zane-zanen hotunan batunci da tozarci ga manzon Allah (SAW) lamarin da ya jawo fushin musulmi a duniya baki daya.

A ranar Lahadin da ta gabata ce ministan harkokin wajen kasar faransa ya gana da babban malamin cibiyar Azhar a birnin Alkahira na Masar, inda suka tattauna kan wannan batu, inda kuma ministan na Faransa ya yi kokarin kwakkwafa fushin musulmi a kan kasar ta Faransa, yayin da shi kuma babban malamin na Azhar ya gargadi Faransa kan cin zarafin manzon Allah (SAW) tare da tabbatar da cewa gwamnatin kasar ta dauki matakin kawo karshen hakan.

 

3934184

 

 

captcha