IQNA

Kungiyar EU Za Ta Bijiro Da Batun Take Hakkokin ‘Yan Adam A Saudiyya A Taron G20

22:57 - November 22, 2020
Lambar Labari: 3485390
Tehran (IQNA) Shugaban kungiyar tarayyar turai ya ce batun take hakkokin bil adama a Saudiyya na daga cikin abin da za su bijiro da shi a  taron G20.

A cikin wani rahoton jaridar Quds Al-arabi ta bayyana cewa, a cikin wani bayani da ya yi ga wakilan kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar kungiyar tarayyar turai, shugaban kungiyar tarayyar turan Charles Michel ya jaddada cewa, batun take hakkokin masu fafutukar kare hakkin bil adama a Saudiyya na daga cikin muhimman abubuwan da za su gabatar a taron G20.

Ya ce akwai dubban mutane da suke cikin kangi a gidajen kuruku da aka garkame su, saboda bayyana ra’ayinsu wanda ya sabawa wan a mahukuntan kasar, kamar yadda kuma  akwai wadanda ake cin zarafinsu sabod rayoyinsu na siyasa, ko saboda babancin fahimta ta akida.

Shugaban kungiyar tarayyar turai an jima ana magana kan yadda masarautar Al Saud take take hakkin ‘yan adam, amma babu wani abu da aka taba yi kan hakan, ya ce a wannan karon kungiyar tarayyar turai za ta yi tsayin daka, domin bin kadun wannan batu.

Majalisar kungiyar tarayyar turai ta aikewa Shugaban kungiyar tarayyar turai Charles Michel da wasika, inda ta bukaci kungiyar EU da ta gabatar da batun take hakkokin bil adama da ake zargin masarautar Saudiyya da aikatawa a gaban taron G20, daga ciki har da batun kisan gillar da masarautar ta yi wa fitaccen dan jarida Jamal Khashoggi.

A yau ne dai ake kammala zaman taron na kungiyar G20 wanda yake gudana ta hanyar hotuann bidiyo, wanda kasar Saudiyya ke jagoranta.

 

3936557

 

 

captcha