IQNA

Zanga-Zangar Mutanen Tunisia Kan Rufe Radio Qur’an Na Kasar

23:41 - December 08, 2020
Lambar Labari: 3485440
Tehran (IQNA) mutane da dama ne suka fito a kan tituna a yau a Tunisia domin nuna rashin amincewa da matakin rufe tashar Radio Quran.

Kafofin yada labarai a kasar Tunisia sun bayar da rahotannin cewa, a yau mutane da dama ne suka fito a kan tituna a birnin Tunis fadar mulkin kasar Tunisia, domin nuna rashin amincewa da matakin rufe tashar Radio Quran na kasar.

Wata kotu ce a kasar ta Tunisia ta bayar da umarnin rufe wannan tashar radio mai farin jinni a wurin mutanen kasar, bisa hujjar cewa lasisin da gidan rediyon yake da shi ya kare, ba tare da an sabunta shi ba.

Saeed Aljuzairi wani dan majalisar dokokin kasar ta Tunisia ne ya bukaci al’umma da su fito domin nuna rashin amincewa da rufe wannan gidan rediyo ta hanyar gudanar da gangami na lumana.

A nata banaren kungiyar kafofin yada labarai masu zaman kansu ta kasar Tunisia ta fitar da bayani, inda take nuna rashin amincewarta da hukuncin kotu na rufe gidan rediyon kur’ani, tare da bayyana hakan a matsayin hukunci mai alaka da siyasa.

Kungiyar ta ce za ta dauki dukkanin matakai na shari’a da doka domin kalubalantar wannan hukunci, domin tabbatar da cewa an baiwa rediyon damar ci gaba da gudanar da shirinsa kamar yadda ya saba.

 

3939684

 

 

 

captcha