IQNA

Kungiyar Hamas Ta Yi Allawadai Da Shigar Da Kayan Kasuwancin Isra’ila A Kasar UAE

22:55 - January 10, 2021
Lambar Labari: 3485543
Tehran kungiyar Hamas ta yi Allawadai da kakkausar murya kan shigar da kayan kasuwancin da Isra’ila take samarwa zuwa kasar hadaddiyar daular larabawa.

Kamfanin dillancin labaran Palestine ya bayar da rahoton cewa, Hazem Kasem kakakin kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ya bayyana cewa, a halin yanzu Isra’ila ta fara shigar da kayan da yahudawa suke samarwa a cikin yankunan Falastinawa da Isra’ila ta mamaye zuwa kasar hadaddiyar daular larabawa UAE.

Ya ce wannan yana a matsayin karfafa gwaiwar Isra’ila ne domin ci gaba da aikinta na mamaya a kan yankunan Falastinawa, haka nan kuma yana a matsayin halasta mata dukkanin ayyukan barna da cin zalun da take yi ne a kan al’ummar Falastinu.

A ‘yan kwanakin da suka gabata, wani babban jami’in gwamnatin yahudawan Isra’ila ya bayyana cewa, kasuwanci tsakanin Isra’ila da UAE zai kai dala biliyan 4 a cikin shekara.

Daga lokacin da gwamnatin kasar UAE ta rattaba hannu tare da Isra’ila watanni hudu da suka gabata kan kulla hulda a tsakaninsu, ya zuwa yanzu kamfanonin Isra’ila da dama ne suka tare a cikin kasar ta hadadiyar daular larabawa suna gudanar da harkokinsu.

3946852

 

 

 

 

captcha