IQNA

Kwamitin Malaman Musulmi Ya Gargadi Gwamnatin Faransa Kan Shiga Cikin Harkokin Musulmi

22:53 - January 24, 2021
Lambar Labari: 3485585
Tehran (IQNA) kwamitin malaman musulmi na duniya ya gargadi gwamnatin kasar Faransa kan yin shigar shugula a cikin harkokin musulmi.

Jaridar Quds Arabi ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ya fitar, kwamitin malaman musulmi na duniya ya gargadi gwamnatin kasar Faransa kan yin shigar shugula a cikin harkokin musulmi na kasar.

  • Babban sakataren kwamitin malaman musulmin na duniya Ali Qarreh Daghi ya bayyana cewa, gwamnatin Faransa ba ta da hurumin da za ta tsara wa musulmi yadda za su gudanar da harkokinsu na addini, domin kuwa lamarin addini batu ne na akida.

Ya ce abin da gwamnatin Faransa take shirin yin a takaita harkokin musulmi da lamurransu na addini a kasar yana a matsayin take hakkokinsu na addini, wanda babu wata doka ta duniya ta amince da hakan.

Daghi ya ce suna kiran gwamnatin Faransa da ta gaggauata dawowa daga rakiyar tunanin da take yi na cewa za ta sanya musulmi su yi addininsu daidai da maharta, ba mahangar da addinin muslunci ya koyar da su ba.

3949634

 

captcha