IQNA

Cibiyar Kur’ani Ta Kasar Jamus Ta Saka Tilawar Karim Mansuri

14:21 - February 01, 2021
Lambar Labari: 3485610
Tehran (IQNA) bababr cibiyar kur’ani ta kasar Jamus da ke da mazauni a birnin Hamburg ta saka tilawar kur’ani da Karim Mansuri ya gabatar.

A kowace shekara a wanann lokaci cibiyar ta kan gudanar da wani majalisi na karatun kur’ani mai tsarki, inda makaranta kur’ani da mahardata sukan halarta daga kasashe daban-daban.

A wanann shekarar sakamon matsalolin da ake fuskanta ta fuskar kiwon lafiya, cibiyar tana gudanar da taron ne ta hanyar yanar gizo, inda ta saka tilawar daya daga cikin fitattun makaranta kur’ani dan kasar Iran Karim Mansuri.

Wannan makaranci ya kasance yana halartar gasar kur’ania  cikin gida tun fiye da shekaru talatin da suka gabata, ya kuma fara wakiltar kasar Iran a tarukan gasar kur’ani na duniya a shekara ta 1991, inda ya zo a mataki na daya  alokuta daban-daban.

3951018

 

 

 

captcha