IQNA

Wani Matashi Dan Kasar Morocco Ya Zana Dakin Ka’abah A Kan Kwarar Shinkafa

23:51 - February 05, 2021
Lambar Labari: 3485620
Tehran (IQNA) wani matashi mai fasahar zane dan kasar Morocco ya zana dakin Ka’abah mai alfarma a kan kwarar shinkafa guda.

Tashar talabijin ta Al-akbariyya ta bayar da rahoton cewa, wani matashi mai fasahar zane dan kasar Morocco mai suna Fu’ad Kibdani, ya zana dakin Ka’abah mai alfarma a kan kwarar shinkafa guda daya.

Wannan matashi musulmi mai shekaru 30 da haihuwa yak ware matuka wajen yin zane-zane masu ban sh’awa da daukar hankali.

Ya bayyana cewa, ya jima yana tunanin zana dakin Ka’abah mai alfarma ta wata hanya ta musamman, wadda za ta zama irinta ta farko a duniya, domin kuwa ya taba yin wani zane mai ban sha’awa a kan kwarar alkama, wanda hakan yasa ya yanke shawarar zana Ka’aba a kan kwarar shinkafa.

Fu’ad ya kara da cewa, babbar manufar zaban wannan salon ita ce, jawo hankalin duniya zuwa ga matsayin wannan wuri mai albarka, wanda shi ne alkiblar dukkanin musulmi na duniya, wanda kuma shi ne aikin fasaha na farko da aka taba yi ta wannan salo.

Ya ce wannan aiki ya dauke shi tsawon lokaci, bayan yin hakuri da kuma sa himma da juriya, a  cikin taimakon Allah ya kammala aikin cikin nasara.

3951956

 

 

 

captcha