IQNA

Martanin Hamas Da Isra’ila Kan Binciken Kotun ICC A Kan Laifukan Yakin Isra’ila A Falastinu

23:51 - March 03, 2021
Lambar Labari: 3485709
Tehran (IQNA) kotun manyan laifuka ta duniya ta sanar da cewa batun bincike kan laifukan yaki da Isra’ila ta tafka a yankunan Falastinawa na nan daram.

Shafin yada labarai na Al’ahad ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ta fitar a yau, kotun manyan laifuka ta duniya ta sanar da cewa tana nan kan bakanta na gudanar da bincike kan laifukan yaki da Isra’ila ta tafka a yankunan Falastinawa.

Hazem Kasim mai magana da yawun kungiyar Hamas ya bayyana cewa, wannan mataki na kotun manyan laifuka ta duniya abin yabawa ne, kuma suna maraba da duk wani bincike da zai taimaka wajen gano irin manyan laifukan da gwamnatin yahudawan Isra’ila take tafkawa a kan al’ummar Falastinu.

Ita ma a nata bangaren gwamnatin kwarya-kwaryan cin gashin kai ta Falastinawa ta yi maraba lale da wannan mataki, inda bayyana cewa tana fatan ci gaba da gudanar da wannan bincike, tare da gurfanar da duk wadanda suke da hannu wajen tafka laifukan yaki daga jami’an gwamnatin yahudawan Isra’ila.

Sai dai a nasa bangaren ministan harkokin wajen gwamnatin yahudawan Gabi Ishkenazi ya bayyana takaicinsa matuka dangane da wannan mataki na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya.

3957502

 

 

 

captcha