IQNA

Jami’an Tsaron Iran Sun Kubutar Da Wani Jirgin Fasinja Na Kasar Da Aka Yi Yunkurin Sacewa

22:07 - March 05, 2021
Lambar Labari: 3485717
Tehran (IQNA) an yi yunkurin sace wani jirgin fasinja a cikin kasar Iran, amma jami’an saron kasar sun watsa shirin.

A cikin wani rahoto na kamfanin dillancin labaran iqna, bangaren jami’an tsaro masu gudanar da ayyukan liken asiri na sararin samaniyar Iran, sun rusa wani shirin sace wani jirgin fasinja a cikin kasar.

Rahoton ya ce wani mutum ne ya yi yunkurin sace jirgin mai lamba 334 wanda ya tashi daga birnin Ahwaz zuwa birnin Mashhad da misalign karfe 10:10 na daren jiya, amma jami’an tsaro na bangaren ayyukan leken asiri na Iran suka bankado lamarin, kuma suka kubutar da jirgi.

Haka nan kuma bayanin jami’an tsaron ya tabbatar da cewa, mutumin ya yi nufin karkata akalar jirgin ne daga cikin kasar ta Iran zuwa daya daga cikin kasashen larabawan yankin tekun fasha.

Bayan faruwar lamarin an saukar da jirgin a garin Isfahan, inda aka canja wa fasinjojin wani jirgi da ya dauke su zuwa birnin Mashhad, dukkanin fasinjojin sun isa birnin Mashhad lami lafiya ba tare da wata matsala ba.

3957715

 

 

 

 

 

 

captcha