A rahoton kamfanin dillancin labaran iqna, bayann kwashe tsawon kwanaki ana kai ruwa rana tsakanin Falastinawa mazauna birnin Quds da kuam jami’an tsaron Isra’ila da suka killace masallacin Aqsa mai alfarma, a jiya jami’an tsaron gwamnatin yahudawan sun bar wuraren da suka ja daga.
Amma a nasu bangaren daruruwan matasan Falastinawa da suke wurin, sun janye dukkanin shingaye da jami’an tsaron Isra’ila suka ajiye a wurin, tare ad shiga cikin masallacin da kuma gudanar da sallolinsu da kuma sauran ayyukan ibadarsu.
Wannan dai yana zuwa ne bayan kwashe tsawon kwanaki tun daga farkon watan Ramadan, yahudawa masu tsatsauran ra’ayi suna tsokanar musulmi, tare da kai farmaki a kansua masallacin Aqsa, kamar yadda kuma jami’an tsaron gwamnatin Isra’ila suke ba su cikakkiyar kariya da tsaro, domin hana Falastinawa mayar da martani a kansu.
Wannan lamari dai ya fusakanci Kakkausan martani daga al’ummomin larabawa a kasashe daban-daban, tare da yin tir da Allawadai da sarakuna gami da shugabannin wasu kasashen larabawan da suka kulla a alaka da Isra’ila a lokutan baya-bayan nan, a daidai lokacin da keta alfarmar wurare masu tsarki na musulmi da ke birnin Quds, da kuma cin zarafin al’ummar Falastinu.